Nigeria: 'A ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara'

Hakkin mallakar hoto zamfara website
Image caption Ana dai zargin gwamnan da rashin zama a yanayin rashin tsaro

Wani tsohon dan majalisar dattawan Najeriya daga jihar Zamfara,Sanata Sa'idu Dansadau, ya rubuta wata doguwar wasika zuwa ga shugaban kasar yana kiran da a ayyana dokar ta baci, a jihar Zamfara.

Senata Dansadau ya yi zargin cewa gwamnan jihar ta Zamfara ya gaza samar da tsaro domin kare rayukan al'ummar jihar wadanda ya ce 'yan fashin shanu ke ci gaba da yi wa kisan kiyashi.

Ko a watan Fabrairu, kungiyar Manoman Nigeria reshen jihar Zamfara sun ce, noma ya faskara a jihar saboda matsalar tsaro.

Baya ga batun rashin tsaro, ana kuma zargin gwamnan jihar da rashin zama, a jihar.

Sai dai gwamnan jihar ya yi watsi da zargin na yin sakaci da aikinsa.