Ali Nuhu ya nemi gafarar mutane

Hakkin mallakar hoto ali nuhu
Image caption Ali Nuhu ya dade yana taka muhimmiyar rawa a Kannywood

Fitaccen jarumin fina-finan Kanyywood, Ali Nuhu, ya bukaci mutane da su yi masa gafara idan ya yi musu laifi, alfarmar watan azumin Ramadana.

Jarumin, wanda ya wallafa sakon a shafinsa na Instagram, ya ce a iya saninsa bai yi wa wani laifi ba, amma duk da haka yana neman gafara saboda ajizancin dan adam.

A cewarsa, "Wannan shi ne satin karshe na wannan watan nan Ramadana. Hakika na san akwai jama'ar Musulmai da dama wadanda wannan shi ne Ramadan dinsu na karshe a nan duniya. Allah shi ne masanin fili da boye, watakila ina cikinsu.''

"Don haka nake kara neman afuwa a wajen dukkan wanda yake da wani hakkinsa a kaina, da kuma duk wanda muka taba samun sabani. Ni dai na yafe wa kowa, kuma ina neman afuwa a wajen kowa da kowa. Allah Ubangijinmu mai afuwa ne, mai rangwame ne. Kuma yana son masu rangwame daga cikin bayinsa. Allah yasa mu dace," in ji Ali Nuhu.

Za a iya cewa Ali Nuhu, wanda ake yi wa kirari da Sarki, ya fi kowanne dan wasan Kannywood mabiya, kasancewarsa mutumin da ya dade yana jan zarensa.