Ana cacar-baki tsakanin Buhari da Saraki

Image caption Saraki ya ce a shirye yake ya sha ɗauri

An soma cacar-baka tsakanin fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban majalisar dattawan kasar Bukola Saraki bayan Saraki ya yi zargin cewa wasu mutane sun kwace ikon tafiyar da kasar daga hannun Shugaba Buhari.

A ranar Litinin ne dai aka gurfanar da Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ikweremadu da wasu mutum biyu a gaban wata kotun Abuja, inda ake zarginsu da yin jabun dokokin majalisar dattawan.

Sai dai sun musanta zargin, kuma alkalin kotun ya bayar da belin su, domin su samu damar halartar ci gaba da shari'a a watan gobe.

Amma a sanarwar da Mista Saraki ya aike wa manema labarai jim kadan bayan barin sa kotun, ya yi zargin cewa wasu mutane sun kwace ikon tafiyar da gwamnatin Shugaba Buhari domin biyan bukatunsu.

Sanarwar ta ce, wannan ''bi-ta-da-kulli'' da ake wa majalisar dokokin na nuna irin matsalar da dimokradiyya ke fuskanta, wadda 'yan kasar suka sha wahala wajen ganin tabbatuwarta.

Buhari ya yi raddi

Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya aike wa manema labarai, ya kalubalanci Mista Saraki da ya bayyana sunayen mutanen da yake zargi da kwace ikon gwamnatin Shugaba Buhari.

A cewarsa, ''Idan Saraki zai bayyana sunayen mutanen da suka kafa wata gwamnati a cikin gwamnatin (Buhari) a nan ne za mu tabbatar da maganar da yake yi ba shifcin-gizo ba ne. Amma yanzu zargi kawai yake yi, wanda bai kamata kowa ya kula da shi ba."

Adesina ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa Ministan shari'a, wanda kuma shi ne babban lauyan gwamnati, damar shigar da karar duk mutumin da ya aikata laifi domin a hukunta shi.

Ya kara da cewa "don haka duk mutumin da ya ce Shugaba Buhari yaron wani ne bai san abin da yake yi ba, domin kuwa ba halayyarsa ba ce."