Cameron zai gana da shugabannin Turai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen Turai sun ce ba sa son tattaunawa kan fitar Biritaniya daga cikinsu

Firai Ministan Biritaniya David Cameron zai gana da shugabannin kasashen Turai a karon farko tun bayan kasarsa ta fita daga Tarayyar Turai.

Mista Cameron zai tattauna da su ne a kan tasirin ficewar Biritaniya daga Tarayyar ta Turai da kuma hanyoyin samun mafita a ganawar da za su iya a birnin Brussels.

A ranar Litinin ne dai shugabannin kasashen Jamus da Faransa da Italiya suka ce babu wata tattaunawa da za su yi a kan fitar Biritaniya daga cikinsu a wannana matakin.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da Sakataren Lafiya na Biritaniya Jeremy Hunt ya yi kira da a gudanar da zaben raba-gardama a karo na biyu na sharudan fitar kasar daga Tarayyar Turan.

A cewarsa, ya kamata a jinkirta fita daga Tarayyar har sai gabanin zaben kasar da za a yi a shekarar 2022.

Shi ne babban jami'in gwamnatin kasar na farko da ya fito fili ya yi wannan kira.