An soma taron tabbatar da tsaro a Niger

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Ana ci gaba da fatattakar 'yan kungiyar ta Boko Haram

A Jamhuriyar Nijar, 'yan majalisar dokoki daga yankin Diffa sun soma ganawa da masu ruwa da tsaki kan yadda za a shawo kan matsalar jhare-haren kungiyar boko Haram a yankin.

Yankin na Diffa da ke makwabtaka da Najeriya dai ya sha fama da hare-haren Boko Haram, kuma akwai 'yan gudun hijirar da rikicin na Boko Haram ya raba da gidajensu, wadanda ke samun mafaka a Diffa.

'yan majaliasar sun yi ganawa ta baya bayan nan ne da shugaba Muhammadu Isufu, inda suka ce burinsu shi ne a samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umar yankinsu.

A cewarsu, hakan ne zai sa manoma su koma ayyukan gona, yayin da su ma 'yan gudun hijira za su koma gidajensu.

Amma hakan ba za ta samu ba har sai an samu cikakken tsaro a kasar, da ma kasashe makwabta irin su Najeriya, in ji 'yan majalisar.