An soke jarrabawar Post UME a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption A ranar Litinin ne ministan ilimi ya fitar da sanarwa a hukumance cewa an soke jarabawar

Gwamnatin Nigeria ta soke yin jarrabawar Post UME, wacce jami'o'i ke yi wa dalibai domin tantance su kafin su ba su gurbin karatu.

A ranar Litinin ne ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya fitar da sanarwa a hukumance cewa an soke jarrabawar.

Hukumar JAMB ce dai take tsara jarabawar ta UME ga dalibai masu neman gurbi a jami'o'i da ma wasu makarantun gaba da sakandare, sanna kuma jami'o'i su shirya Post UME domin kara tantance daliban.

JAMB na karbar N 5000 daga wurin kownane dalibi don yin jarrabawar, yayin da jami'o'in suke karbar tsakanin N2000 zuwa N60000 daga masu neman gurabe a matsayin kudin da za su biya bayan jarrabawar ta UTME.