Za a janye wasu motocin Toyota daga Amurka

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane na son hawa motocin Toyota

Kamfanin kera motoci na Toyota mallakar kasar Japan ya sanar da cewa zai yi wa kusan motocinsa dubu dari biyar kiranye daga Amurka saboda matsalar balan-balan din da ke bai wa mutum kariya a lokacin hadari, wato Airbag.

Kamfanin Toyota ya ce matsalar ka iya janyo hayaki a cikin motar lamarin da zai sanya karuwar kurje motocin.

Motocin da za a yi wa kiranye dai sun hada da wadanda aka kera tsakanin shekarar 2010 zuwa 2012, ciki kuwa har da motar alfarma ta Lexus.

Wannan shi ne kiranye na baya-bayan nan da fitaccen kamfanin ya yi, kuma Toyota ya ce ba shi da masaniya game da matsalar sai kwanan nan.