'Mutum 41 aka kashe a harin Istanbul'

Hakkin mallakar hoto GETTY
Image caption An umarci fasinjoji su kaurace wa filin jirgin Santanbul.

Gwamnatin kasar Turkiyya ta ce mutanen da suka mutu sakamakon harin bama-baman da aka kai a filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul sun karu zuwa 41.

Gwamnan birnin ya ce 13 daga cikinsu 'yan kasashen waje ne, yana mai cewa mutum 239 suka jikkata.

Mahara uku ne a cikin motar tasi suka kai harin, inda suka yi ta bude wuta a kofar shiga filin jirgin ranar Tlata.

Maharan sun tarwatsa kan su bayan 'yan sanda sun bude musu wuta.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoan, ya dora alhakin harin kuna- bakin-wake da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 36 a filin jirgin birnin Santanbul, akan kungiyar mayakan IS.

Ya ce an kai harin ne da manufar bata sunan Turkiyya a idanun duniya ta hanyar zubar da jinin mutanen.

An tsayar da hada-hadar jirage sannan aka umarci mutane su kaurace wa filin jirgin.

Turkiyya dai na fuskantar hare-hare daga kungiyar IS da kuma mayakan sa-kai na kabilar Kurdawa.

Wadannan hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da ludayin filin jirgin yake kan dawo.

A 2015 ne dai filin jirgin na Attaturk ya zamo uku ma fi yawan sauka da tashin jirage a nahiyar turai.

Wato ya biyo bayan filin jirgin Heathrow da ke birnin London da na Charles de Gaulle na birnin Paris.

Fiye da fasinjoji miliyan 61 ne suka sauka ko suka tashi daga filin a shekarar 2015.