An kama ma'aikatan jarida a Zambia

Image caption Gidan jaridar ya ce ana son hana fadin albarkacin baki

'Yan sanda a kasar Zambia sun kama Editan babbar jaridar kasar, The Post, da matarsa da kuma mukaddashin manajan gidan jaridar.

A makon jiya ne hukumar karbar harajin Zambia ta rufe ofishin jaridar a kan bashin miliyoyin daloli da ta ce tana bin, wadanda suka ki biya.

Sai dai hukumar gidan jaridar ta ce ba batun haraji ne ya sanya aka rufe shi ba, tana mai cewa an yi hakan ne domin a kawo cikas a 'yancin fadar albarkacin bakin jama'a a daidai lokacin da ake shirin yin babban zaben kasar a watan Agusta mai zuwa.

An dai cafke mutum ukun ne a lokacin da suke shiga gidan jaridar a a birnin Lusaka, kuma cikin zarge-zargen da ake yi musu har da laifin aikata mugun laifi.