'Yan achaba sun sake mamaye Kaduna

Image caption An dai hana sana'ar achaba a Kaduna a lokacin gwamnatin PDP da ta shude.

A Kaduna da ke arewacin Najeriya, wasu 'yan jihar suna alakanta dawowar sana'ar achaba da yawaitar muggan laifuffuka.

Ana dai samun yawaitar aikata manyan laifuka kamar hare-hare da fashi da makami.

A makon nan ne dai wasu 'yan bindiga guda biyu a kan babur suka kai wa wasu mutane hari, kuma suka harbe mutum biyar har lahira sannan suka jikkata hudu.

Kimanin shekara biyu kenan dai gwamnatin jihar Kaduna ta haramta sana'ar achaba.