Shugabannin EU na taro ba Cameron

Image caption Mista Cameron ya ce yana da muhimmanci Birtaniya da Tarayyar Turai su ci gaba da hulda ta fuskar cinikayya da tsaro

Shugabannin kasashen Tarayyar Turai sun shiga kwana na biyu na taron da suke yi a Brussels, amma kuma ba tare da Firai Ministan Birtaniya, David Cameron ba, bayan kasar ta zabi ficewa daga kungiyar.

Wasu kasashe 27 na kungiyar za su tattauna a kan shirin da Biritaniya take yi na ficewa daga tarayyar Turai, yayin da wannan ne karo na farko da Birtaniyar ta kasance ba ta cikin kasashen da za su kulla yarjejeniya a shekara 40.

A ranar Talata ne dai Mista Cameron ya ce yana da muhimmanci Birtaniya da Tarayyar Turai su ci gaba da hulda ta fuskar cinikayya da tsaro.

Shugabar gwamantin Jamus, Angela Merkel, ta bukaci kungiyar da ta "girmama sakamakon" kuri'ar raba-gardamar da Biritaniyar ta kada.

Misis Merkel da wasu shugabannin sun kara kira da Biritaniya ta tsara shirinta na fita nan da ba da dadewa ba.