Kuraye sun cinye wani mutum a Kenya

Image caption Su ma Zakuna sun cinye ragiwar naman mutumin da Kuraye suka rage

Ana tsammanin Kuraye sun kashe wani mutum tare da cinye kusan dukkan naman jikinsa a kasar Kenya.

Shugaban gundumar da abin ya faru Cif Vincent Leipa, ya sanarwa da al'ummarsa cewa wannan ne karo na biyu da irin wannan ta taba faruwa a wannan yanki da ke garin Ongata Rongai.

Al'amarin ya faru ne ranar Juma'a da daddare a lokacin da mutumin ke kan hanyar komawa gidansa a garin wanda ke kusa da gandun namun daji na Nairobi babban birnin kasar.

Kazalika, wata jaridar kasar ta ruwaito cewa wasu gungun Zakuna sun karasa cinye sauran naman jikin mutumin.

Tuni dai 'yan sanda suka kwashe abin da ya yi saura na jikin nasa a ranar Talata da daddare.