Malami ya taimaka wa ɗalibarsa da goyo

Image caption Malamin dai ya ce ya yi haka ne don uwar yaron ta rubuta jarrabawa a cikin natsuwa

Wani malamin jami'a a ƙasar Ivory Coast na ta shan yabo da jinjina a kafafen sada zumunta na intanet, bayan da wani hotonsa da yake goye da jaririya ya bazu a shafin intanet.

Malamin dai ya karbi jaririyar wata ɗalibarsa ne da ke ta faman tsala kuka a yayin da ake rubuta jarrabawa

Ya shaida wa wakilin BBC Amadou Diallo cewa dalilin da ya sa ya goya jaririyar shi ne domin mahaifiyar yarinyar ta samu damar yin jarrabawarta a natse.

"Matar ta shiga ɗakin karatun da jariri, amma kuma sai ta fito, tana ta kai da kawowa. Na lura ba ta cikin hayyacinta sosai. Sai na yi tunanin watakila tana da wani abin da ke damunta,'' in ji malamin.

Ya ƙara da cewa, ''Sai na matsa kusa da ita kuma na tambaye ta ko tana buƙatar taimako? Abin ya ba ta mamaki, sai na sake tambayarta ko zan iya rike mata jaririyar? Sai ta ce eh, sai na karɓa.''

Da wakilin BBC ya tambaye shi ko ya ya sauran ɗaliban suka ji da wannan salo nasa? Sai ya ce, ''Sun yi mamaki, sun yi matuƙar mamaki. Da farko dariya suka fara yi, amma daga bisani suka fara cewa wannan uba ne na gari, namijin ƙwarai ne, abin koyi ne.''

Ɗaliban ne dai suka yi ta ɗaukar hotunan malamin goye da yarinyar, saboda a cewarsu abin ya burge su.

A iya cewa wannan labari ya bazu ne tamkar wutar daji a kasar ta Ivory Coast saboda ba kasafai ake ganin namiji da goyo a bayansa ba a ƙasashen Afirka.