'Dimokradiyya bata zauna ba a Myanmar'

Shugaban Myanmar Hakkin mallakar hoto Myanmar President Office
Image caption Sojoji sun dade su na mulki a kasar Myanmar

Gwamnatin kasar Myanmar ta amince cewa har yanzu kasar bata cika ka'i'dojin Dimokradiyya ba.

Ministan yada labaran kasar Pe Mint ne ya sanar da haka a wata hira da BBC, inda ya ce har yanzu kasar bata farfado daga mulkin da sojoji suka yi shekaru masu yawa suna yi ba.

Karkashin kundin tsarin mulkin kasar, wanda Aung San Suu Kyi ta jagoranta, dole ne a raba madafun iko da sojojin kasar da suke rike da kashi 20 cikin 100 na kujerun majalisar Dokoki.

An kafa gwamnatin ne bayan nasarar da jam'iyyar Natinal League for Democracy ta Aung San Suu Kyi ta yi a zaben da aka yi watan Nuwambar 2015.