Yadda na fara sha'awar tukin jirgi — Al-Hawsawi

Ku saurari Hira da Nawal Al-Hawsawi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Nawal Al-Hawsawi wata Bahaushiya ce amma 'yar asalin Saudiyya da ta kafa tarihi.

Ita ce mace bakar fata ta farko da ta samu lasisin tuka jirgin sama a Saudiyya.

Baya ga wannan bajintar, Nawal, kwararriya ce wajen bayar da shawarwari ga masu larurar tabin hankali.

To a kwanakin baya, ta kawo mana ziyara Sashen Hausa na BBC, a London inda Jimeh Saleh ya yi hira da ita.

Ganin cewa Hausar Nawal na cijewa, mun kuma gayyato Mahaifinta cikin hirar amma ta waya.

Image caption Nawal AlHausawiy tare da Jimeh Saleh a lokacin da suke tattaunawa.

Nawal Al-Hawsawi dai tana kuma yaki da nuna bambancin launin fata. Yanzu wannan kallabi tsakanin rawunan, ta zama gwarzuwa abar misali ga mata da dama a Saudiyya dama sauran kasashen duniya.

An sha sa sunanta a jerin mata dari da suka fi tasiri a duniya.

Image caption Wata 'yar Najeriya ce ta karfafa mata gwiwa