Shin yaya za a yi Sallar bana a Nijar?

Muhammadou Issoufou
Image caption Iyaye kan hakura da kayan sallah dan 'ya'yan su su sanya.

A Jamhuriyar Nijar, yayin da ya rage kwanaki kalilan kafin ranar karamar Sallah, hankulan jama'a sun karkata ne wajen samun tufafin sallar, musammam mata da yara kanana.

Sai dai wasu na cewa Sallar ta bana ta zo cikin wani lokaci na rashin kudi wanda hakan ya sa ba karamin aiki ba ne ga magidanci ya tufatar da iyalin nasa.

Wakilinmu Baro Arzika, wanda ya ziyarci wata kasuwar baje-koli a Yamai domin jin yadda al'amurran ke gudana, ya ce mutane da dama sun je kasuwar.

Yawancin mutanen da suka je sayayya dai sun shaida masa kaya sun yi tsada, ga shi kuma babu kudi a hannun mutane.

Don haka iyaye ba su da mu da dinkawa kan su tufafin sallah ba, sun mayar da hankali ne a kan yara.

Matsin tattalin arzikin ya kai har wasu na sayar da kadararorinsu domin sama wa yara tufafin Sallah.