MDD ta ce yara na cikin garari a Iraqi

Yaran Iraqi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara na cikin mawuyacin hali a Iraqi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce karuwar tashe-tashen hankali a kasar Iraqi ta sanya rayuwar kashi daya cikin biyar na yaran kasar cikin hadari.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta ce fiye da shekaru biyu da rabi kenan kusan yara Dubu daya da dari biyar aka sace, yawancin su kuma an tilasta musu shiga yaki, wasu kuma ana cin zarafin su ta hanyar lalata da su.

UNICEF ta ce kusan kashi 10 cikin 100 na yaran Iraqi ne suka tsere daga gidajen su saboda rikicin da ake yi a kasar, kuma yaran na cikin tsananin bukatar taimako.