Facebook ya sa budurwa tafiya neman saurayinta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Budurwar dai ta ahdu da saurayin a shafin Facebook

'Yan sanda suna tsare da wata yarinya 'yar shekara 14 a Bangladesh, wadda suka kama a kokarinta na barin kasar don zuwa Pakistan ta ga saurayinta.

Yarinyar wadda take da zama a babban birnin Bagladesh Dhaka, ta hadu da yaron ne a shafin Facebook.

Ta shirya guduwa ne ta bin iyakar Indiya ta tsallaka zuwa Pakistan domin haduwa da saurayin.

Budurwar dai ta sace gwala-gwalan mahaifiyarta domin guduwa da su, kafin daga bisani jami'an tsaron kan iyaka suka tare ta a garin Rangpur da ke arewacin kasar.