Wata uwa za tai amfani da kwan haihuwar 'yarta

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Matar na son ta haifi jikokinta ne da kanta bayan mutuwar 'yar tata

Wata mata 'yar shekara 60 a Birtaniya ta samu nasara a wata shari'a da aka bata izinin amfani da kwan haihuwar marigayiyar 'yarta da aka dade ana adanawa, don ta haifi jikanta da kanta.

'Yar matar dai ta adana kwan haihuwarta ne a lokacin da take da shekara 23, bayan da aka ce tana da cutar kansa.

Ta mutu bayan shekara biyar da yin hakan, inda ta furta cewa tana so mahaifiyarta ta yi amfani da kwan haihuwar don ta haifar mata 'ya'yanta, amma bata bari a rubuce ba.

Hukumar kula da kwayayen haihuwar dan adam ta Birtaniya, ta hana a dauko kwayayen haihuwar daga ma'adanarsu, hukuncin da wata babbar kotu ta goyi bayansa.

Amma kotun koli ta sauya hukuncin, inda ta bayar da hujjar cewa akwai kwararan shaidu na wasiyyar da 'yar ta bari.