An kashe mutum 10 a masallacin Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani dan kunar-bakin wake ya tayar da bama-baman da ke jikinsa a kusa da wani Masallaci a arewacin Kamaru, lamnarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum goma.

Jami'an tsaro sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa mutumin ya tayar da bama-baman ne a lokacin da Musulmi ke shirin yin sallah a wani tanti da ke garin Djakana bayan sun sha ruwa.

Wani soja ya ce dan kunar-bakinwaken yaro ne karami.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hari a yankin.