Za a rufe babban gidan jaridar Gabashin Afirka

Image caption Za a kori ma'aikata da dama

Za a rufe babban rukunin gidajen jaridar Nation Media Group da ke Gabashin Afirka.

Wata sanarwa da masu rukunin gidajen jaridar suka fitar ya ce zai rufe uku daga cikin gidajen rediyonsa (Nation FM, QFM da KFM) da gidan talabijin daya (QTV).

Hakan dai zai sa mutane da dama su rasa ayyukansu.

Rukunin gidajen jaridar na The Nation Group ya ce yana shirin sabunta ayykansa ta yadda zai dace da zamani, inda zai mayar da hankali a kan fasahar sadarwa ta zamani musamman watsa labarai ta wayoyin salula.

Rukunin gidajen jaridar shi ne kamfanin da ke wallafa jarida mai zaman kanta mafi girma a Kenya, The Nation, da The East African wacce ta fi farin jini a yankin.

Aga Khan ne ya kafa rukunin gidajen jaridar kusan shekara sittin da suka wuce.