Metuh na goyon bayan Buhari kan yaki da rashawa

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Hukumar EFCC ce take tuhumar Mista Metuh

Kakakin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Cif Olisa Metuh, ya ce a shirye yake mayar wa gwamnatin kasar naira miliyan 400 da ake zarginsa da sacewa.

Mista Metuh ya bayyana hakan ne a wata sanawa da lauya mai kare shi a gaban kuliya ya aike wa manema labarai.

Sanarwar ta ce a Mista Metuh bai san tushen kudin ba, wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi umarni a bashi bayan ya gabatar masa da irin ayyukan da zai yi da su na jam'iyya.

Ta kuma ce tun a karon farko da aka bukaci ganinsa a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro a watan Disambar 2015, ya ce zai mayar da kudin in har na gwamnati ne.

Mista Metuh ya ce kuma tun daga lokacin ne ya fara neman 'yan uwa da abokan arziki su harhada masa abin da ya sauwaka domin dawo da kudin, duk da cewa tuni ya bi umarnin tsohon shugaban kasar wajen gabatar da ayyukan da aka sa shi ya yi da kudin.

Sanarwar ta kara da cewa, ''Dawo da kudin da zai yi na nuna goyon bayansa kan yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi, da kuma nuna gaskiyarsa da kuma kare mutuncinsa.''

Lauyan nasa Onyechi Ikpeazu, ya ce a don haka yana da matukar muhimmanci a bayyana yadda Mista Metuh ke matukar goyon bayan yaki da cin hanci ta yadda za a yi nasara har komai ya dawo kan doka da tsari.

A watan Janairun 2016 ne hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, ta kai shi gaban kuliya bisa zargin ya karbi Naira miliyan 400 daga hannun Kanar Sambo Dasuki a cikin kudin makamai da ake zargin sun karkatar da su.