An soke zaben shugaban kasar Austria

Image caption Za a sake zaben Austria

Babbar kotun Austria ta soke zaben shugaban kasar wanda jam'iyya mai ra'ayin-rikau ta The Freedom Party ta sha kaye.

Jam'iyyar ta kalubalanci sakamakon zaben a kotu, tana mai cewa an yi cuwa-cuwar kuri'un da aka aike ta gidajen waya.

Dan takarar The Freedom Party, Norbert Hofer, ya sha kaye a hannun tsohon shugaban Greens, Alexander Van der Bellen, da kasa da kashi daya cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Yanzu dai za a sake zabe.

A lokacin da yake soke zaben, alkalin kotun, Gerhard Holzinger, ya ce "an amince da korafin da shugaban jam'iyyar Freedom Party Heinz-Christian Strache kan zaben da aka gudanar ranar 22 ga watan Mayu, don haka an soke zaben."

Mr Hofer ne zai zama dan takarar jam'iyya mai ra'ayin-rikau na farko a Turai da ya zama shugaban kasa idan aka zabe shi.