Nijar: An kori likitoci daga aiki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Gwamnati na zargin likitocin da kin zuwa aiki amma suna karbar albashi

A Jamhuriyar Nijar wata takaddama ta kunno kai tsakanin ma'aikatar kiwon lafiya da wasu Likitoci sama da 30 sakamakon matakin da gwamnati ta dauka na korarsu daga aiki.

Gwamnatin dai na zargin likitocin ne da kaurace wa wuraren aikinsu, amma kungiyar Likitocin kasar ta ce ba ta yarda ba.

Gwamnatin dai ta gudanar da bincike ne kafin ta dauki wannan mataki, inda ta bayyana cewa, wasu daga cikin likitocin sun shafe watanni da dama ba tare da sunje aiki ba kuma su na karbar albashi.

Sai dai kuma kungiyar likitocin ta musanta zargin da gwamnati ke yiwa 'ya'yan na ta, inda ta ce karin karatu suka je ba haka kawai suke kin zuwa aiki ba.