Talaka zai sha wuya saboda faɗan Buhari da Saraki

Dambarwa tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dattijaN Najeriya ta kara zafafa, bayan gaza bayyanar da ministan shari'ar kasar, Abubakar Malami ya yi a zauren majalisar wadda ta gayyace shi kan batun karar da ya shigar da Sanata Bukola Saraki da Ike Ekwerenmadu bisa zargin yin jabun dokoki.

Ministan dai ya aika wani jami'i ne don ya wakilce shi maimakon zuwa da kansa, lamarin da ya fusata 'yan majalisar.

Wasu dai na ganin irin wannan dambarwa za ta dauke hankalin gwamnati daga yi wa talakawa aiki.

Farfesa Kamilu Sani Fagge masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero ta Kano, ya yi wa Mukhtar Adamu Bawa karin haske game da yadda ya ke kallon wannan dambarwa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti