An sace mataimakin jakadan Saliyo a Nigeria

Image caption Har yanzu babu cikakken bayani kan yadda aka sace jami'an

Rahotanni daga Nigeria na cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da jama'a ne sun sace mataimakin jakadan Saliyo a Nigeria, Manjo Janar Nelson Williams mai ritaya.

A ranar Alhamis ne aka ce ya baro Abuja domin zuwa Kaduna domin halartar bikin yaye dalibai sojoji a Jaji.

Akwai rahotanin da ke cewa masu garkuwar da jama'a sun bukaci a biya miliyoyin daloli kafin a sako shi.

Sace mutane da yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa dai ba sabon abu ba ne a kasar.