Amurka na binciken hadarin mota marar matuki

Hakkin mallakar hoto Getty

Narr: Mahukunta a Amurka sun fara gudanar da bincike a kan hadarin da wata mota marar matuki ta yi, hadarin da shi ne karon farko da mutum guda ya mutu a motar.

Motar dai tana amfani ne da lantarki, kuma tana iya yin kiliya ko sauya hanya da kanta.

A watan Mayun da ya wuce ne motar ta yi hadari a jihar Florida lokacin da ta yi karo da wata Tantan, kuma a lokacin Direbanta na cikin motar amma da shi da ita duka ba su hangi Tantan din ba.

Kamfanin Tesla, wanda ya kera motar ya ce ya kamata deriban motar ya matsa na'urar da za ta ba shi damar karbar ragamar tuki a duk lokacin da yake ciki, maimakon ya sakankance ya kyale ta tana tuka kanta, saboda a cewar kamfanin, an yi na'urar sararrafa motar don taimakawa ne kawai.

Sai dai wani masanin fasaha, mai suna Ben Parr, ya ce kamfanin ya ci da zuci saboda " karo daya kamfanin Tesla ya jefa motarsa cikin jama'a sabanin hanyar da kamfanin Google ya bi, wanda har yanzu yana kan jarraba motarsa"