An kashe mutane 20 a harin Bangladesh

Hakkin mallakar hoto Getty

Jami'an tsaro a Bangladesh sun ce an kashe mutane 20, akasarinsu 'yan kasashen waje, a wani harin da aka kai a gidan shan shayi a Dhaka, babban birnin kasar.

An kashe su ne bayan an yi garkuwa dasu a wajen shan shayin wanda ke wata unguwar masu galihu a Dhakan.

Daga cikin wadanda aka kashen harda 'yan Italiya, da 'yan Japan, 'yan Korea ta Kudu da Indiyawa da kuma 'yan kasar ta Bangladesh.

Wani kakakin soji ya ce an ceto mutane 13 daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasun, bayan da jami'an tsaro suka falma gidan abincin, domin kawo karshen mamaye shin da 'yan bindiga suka yi tun ranar Juma'a da dare.

Ya kuma ce an kashe shidda daga cikin wadanda suka kai harin, an kuma kama dayansu.

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai harin.

A wani jawabin da ta yi a gidan talebijin, Firaministan Bangladeshin, Sheikh Hasina, ta sha alwashin kauda ta'addanci a kasar.

Karin bayani