BH: Mutane 500 aka kashe a Kamaru

Mayakan kungiyar Boko Haran Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Kungiyar Boko Haram

Kungiyar Amnesty International a wani rahoton da ta fitar ta bayyana cewa Kungiyar Boko Haram ta hallaka rayukan fararen hula 480 a cikin shekara guda a Kamaru.

Daga watan Yulin shekara ta 2015 zuwa ta 2016, kungiyar Boko Haram a cewar Amnesty ta aiwatar da kai hare-hare 200.

Ta kuma ce Kusan 40 na kunar bakin wake dukkansu kuma a lardin arewa mai nisa.

Dangane da haka, kungiyar Amnesty International ta yi kira ga dakarun tsaro da su dauki dukkanin matakan da suka wajaba wurin ganin sun kare rayukan jama'a, su kuma mutunta dokoki.

Kungiyar kuma ta kammala da cewa, wadanda suka take hakkokin bani adam da sunan kare rayukan jama'a, a gurfanar da su a gaban kotu, a yanke musu hukunci, amma ba na ratayesu ba.