Jamus ta doke Italiya a wasan shiga dab da na karshe

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kasar Jamus ta doke Italiya a wasan gab da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafa na Turai, a wani bugun fenariti mai ta da hankali.

Gaban kowane bangare ya yi ta faduwa ne sakamakon barar da fenarti uku-uku a jere da 'yan wasan dukkan bangarori biyun suka yi.

Ana wannan yanayin ne Golan Jamus, Manuel Neuer ya yi katarin kade fenariti guda, yayin da Jonas Hector ya zura nasa kwallon a ragar Italiya, lamarin da ya ba wa Jamus nasara.