Fursunoni na bukatar agaji

A Najeriya, wasu yan kasar na kira ga masu hannu da shuni da su kai agaji gidajen yari domin taimaka wa wadanda ke tsare sakamakon tarar da ba ta taka-kara-ta-karya ba.

Rahotanni dai na nuna cewa akwai mutane da kan shafe watanni ko ma shekaru a gidajen yari saboda gazawar da suke yi wajen biyan tarar da wasu lokuta ba ta wuce dubu uku ba.

Wata kungiyar sa-kai ta agaza wajen 'yanta irin wadannan fursunonin sama da 30 a wasu gidajen yarin da ke jihar Kaduna.

Alhaji Sirajo Halilu, ya ja hankalin masu hannu da shuni da su rinka taimakawa fursunonin da tarar da ake binsu bata taka kara ta karya ba musamman ma a cikin watan Ramadan.

Ga dai abinda ya ke cewa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti