'Yan bindiga sun kashe dan majalisar Oyo

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan bindiga sun kashe shugaban kwamitin tsaro da yada labarai na Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Mista Gideon Aremu, a kudu maso yammacin Najeriya.

Kamfanin dillacin labaran Najeriyar ya ruwaito cewa 'yan bindigar sun harbe Mista Aremu har lahira a lokacin da zai shiga gidansa a Ibadan da misalin karfe tara na dare a ranar Juma'a.

Matarsa ta bude masa kofar gidan ne zai shiga sai 'yan bindigar su biyu, wadanda suka je akan babura, su ka harbe shi.

Rahoton ya ce sai da 'yan bidigar suka tsaya suka tabbatar da cewa ya mutu kafin su tafi, kuma babu abin da suka dauka daga wajen shi sai wayar salularsa.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Mista Adekunle Ajisebutu, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ya ba da umurnin a gudanar da kwakwkwaran bincike.

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Mista Musah Abdul-Wasi, ya ce kashe Aremu abu ne mai tsoratarwa, kuma babbar asara ce ga jihar da ma Najeriya baki daya.

Ya ce da ba'a kashe shi ba, da a makon gobe ne Mista Aremu zai yi bikin karbar digir-gir (wato PhD) dinsa daga Jami'ar Ilorin.