Mutane 18 sun ji raunuka a Saudiyya

Makka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masallacin Makka

Kafofin watsa labarai a kasar Saudiyya sun ce masu aikin umrah 18 suka ji raunuka a turmustutsin da ya faru a masallacin Makka.

Mutane da dama suka taru a cikin masallacin domin yin ibada a daren da ya fi kowane daraja a azumin watan Ramadan.

Wani jami'in lafiya ya ce an bai wa wadanda suka ji raunuka magani a wurin da lamarin ya faru.

Haka kuma lamarin na zuwa ne bayan da hukumomin kasar su ke cigaba da bulo da sabbin matakan kiyayewa a aikin hajjin bana da za a yi a watan Satumba mai zuwa.

Mutane fiye da dubu biyu suka rasu a turmutsutsin da ya faru a bara.