Avengers ta ce ta kai sabbin hare-hare

avengers

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a farkon shekarar nan kungiyar Avengers ta fara kai hare-hare kan bututan mai

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Niger Delta Avengers NDA, a Najeriya, ta sanar da kai wasu manyan hare-hare kan tasoshin man fetur da iskar gas a kasar.

Kungiyar ta sanar da kai wadannan hare-hare ne a shafinta na Twitter a ranar Asabar da daddare.

'Yan kungiyar sun ce sun kai hare-haren ne kan tasoshin man fetur na kamfanin mai na kasar, wato NNPC, da kuma na kamfanin Chevron.

Sun kuma ce sun lalata wani bututun mai mallakin NNPC, wanda ke tura danyen mai zuwa matatar man fetur ta Warri a jihar Delta, a ranar Juma'a da daddare.

Daga ranar Asabar da daddare zuwa ranar Lahadi da safe dai kungiyar ta ce ta kai manyan hare-hare har hudu inda ta lalata bututan mai duk a jihar ta Delta.

'Karin bayani'

A shafinta na Twitter, kungiyar Avengers ta ce da misalin karfe 11:26 na dare a ranar Asabar ta lalata wasu muhimman bututan kamfanin NNPC guda biyu da ke kusa da tashar Batan a jihar Delta.

Da misalin karfe 1:15 na tsakar daren Asabar din kuma ta lalata manyan rijiyoyin mai na kamfanin Chevron guda biyu masu lamba 7 da 8 da ke kusa da tashar Abiteye a jihar Deltan.

NDA ta kuma ce tawaga daya ce ta kai dukkan hare-haren.

Babu dai wata sanarwar hukumomi a Najeriya kan lamarin.