Iraki: Bam ya hallaka mutum 119 a gidan abinci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne hari mafi muni da aka kai a Iraki cikin 2016

Hukumomin a Iraki sun ce akalla mutane 119 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin wasu bama-bamai biyu a Bagadaza, babban birnin kasar, yayin da wasu fiye da 150 suka jikkata.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken a mota kusa da kantin sayar da abinci da ke tsakiyar yankin Karada, inda a nan ne mutane suka fi mutuwa.

Bam na biyu ya tashi ne a arewacin Bagadaza, inda mutane biyar suka mutu a can.

Sharhi kan hare-haren

Bama-baman sun tashi ne a yankin Karada da goshin asuba, lokacin da mutane suka taru a kantin sayar da abinci domin yin sahur.

Kantin na kan titin da mabiya shi'a suka fi yawa ne wanda kuma baya rabuwa da mutane masu kai kawo don sayen abin kai wa baka.

Firai ministan kasar Hydar Al abadi ya hadu fushin mutne yayin da yayi kokarin ziyatar wajen. Jama'a sun yi ta jifan motocinsa da duwatsu da sanduna.

Haka kuma mutane sun yi ta bayyana bacin ransu intanet.

Masu zamba ta intanet sun kuma samu nasarar yin ktse a shafin intanet na ma'aikatar harkokin cikin gidan kasra, inda suka saka hoton wani yaro da ya mutu.

Bam na biyu ya tashi ne da kusan tsakar daren Asabar a yankin da nan ma mabiya shi'a ne suka fi yawa a birnin na Bagadaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar.

Wannan hari dai shi ne mafi muni da aka kai birnin Bagadaza cikin shekarar nan.

Harin na zuwa ne mako guda bayan da dakarun kasar suka kwato ikon birnin Fallujah daga hannun mayakan IS.