Kano: An yi wa 'yan daba tayin afuwa

Hakkin mallakar hoto Getty

A Najeriya, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kaddamar wani sabon yaki da ayyukan 'yan daba ta hanyar wani shiri mai suna Operation share-daba.

Wani bangare na shirin na karfafa gwiwar 'yan daba su ajiye makamansu, su rungumi zaman lafiya, inda za su ci gajiyar afuwa, matukar babu wani zargin aikata babban laifi a kansu.

Mazauna unguwanni da dama ne dai ke kokawa da ayyukan 'yan daba da suka fitini mutanen gari wadanda ba-su-ji-ba-ba-su-gani-ba ta hanyar auka musu da sara da suka, abin da a wani lokaci kan haddasa asarar rayukan jama'a.

Ganin yadda ayyukan 'yan daban ya yiwa a wasu unguwanni a jihar ta Kano, rundunar 'yan sandan jihar ta bullo da wannan shiri.

Rundunar 'yan sandan ta ce shirin wata wuka ce mai baki biyu.