Matashi ya kera tantan a Nigeria

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Tuni dai aka jarraba motar domin tabbatar da ingancinta.

A Najeriya, wani matashi dan jihar Benue ya kirkiro wata karamar motar noma, wato Tarakata ko Tantan wadda dukkan kayan da aka yi amfani da shi wajen kera ta a Najeriya aka yi shi.

Shi dai matashin, mai suna Terfa Addingi, ya ce ya kirkiri Taraktar ne domin saukaka wa kananan manoma hidimar gona.

Tuni dai aka jarraba motar domin tabbatar da ingancinta.

Terfa Addingi ya ce yana fatan samun tallafi domin fadada kamfanin da zai rika kera Taraktar, wanda ta hakan yake fatan samar da aikin yi ga wasu matasan.

Motar da matashin ya kirkira mai saukin sarrafawa ce wadda mata ma za su iya tuka ta, kuma ya dauki tsawon watan biyu ne kawai yana hada ta.