Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 180 a China

Hakkin mallakar hoto Getty

Fiye da mutum 180 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da kogin Yangtze na kasar China ya yi bayan an yi ruwan sama kamar da bakin-kwarya.

An tafka ruwan ne dai a larduna bakwai, inda aka rika yin tsawa wacce ta karade tsawon kilomita 1,600 a tsakiya da kudancin kasar.

Kimanin mutum 45 sun bata kuma jami'ai sun ce lamarin ya shafi mutum miliyan 33.

Ruwan ya tumbuke taragwan jiragen kasa da mamaye manyan hanyoyi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto Reuters