Ana makoki a Iraqi bayan kisan mutum 165

Hakkin mallakar hoto

Gwamnatin kasar Iraqi ta ayyana makokin kwana uku a fadin kasar bayan wani harin bama-bamai da aka kai a birnin Baghdaza ya halaka mutum 165 kana ya jikkata mutum 225.

Wata mota ce dai makare da bama-bamai ta tashi a lardin Karrada a lokacin da mutane ke sayen kayan abinci a kantuna domin yin buda-baki.

Masu bayar da agaji sun ce sun iyali da dama sun rasa daukacin 'yan uwansu kuma akasarin mutanen da lamarin ya shafa sun yi mummunan konewa ta yadda ba za a iya gane su ba.

Kungiyar IS dai ta dauki alhakin kai harin.

Firai ministan kasar Haider al-Abadi ya ziyarci iyalan mutanen da lamarin ya shafa a yankunan da 'yan Shia suka fi yawa ranar Lahadi, sai dai mutane da dama sun nuna masa fushinsu.

Daga bisani ne ofishinsa ya fitar da sanarwar yin makokin kwana uku, yana mai cewa Mr Abadi ya fahimci dalilin da ya sa mutane suka yi matukar fusata.