Netanyahu na ziyara a Afrika

Image caption Mista Netanyahu ya ce Isra'ila za ta bayar da tallafin $13m ga Uganda da sauran kasashen Gabashin Afrika

Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya fara wata ziyara a kasar Uganda.

A yayin ziyarar tasa a nahiyar, Mista Netanyahu zai kuma je kasashen Kenya da Habasha da Rwanda.

Mista Netanyahu ya fara ziyarar da Uganda ne saboda ana bikin tunawa da shekaru 40 da kai harin Entebbe, inda kwamandojin sojin Isra'ila suka kai harin domin sakin fasinjojin wani jirgin sama da aka tilastawa, sauka a filin jiragen sama na Uganda.

Dan uwan Firai ministan, Yonatan Netanyahu, na daga cikin wadanda aka kashe a kokarin kubutar da su.

Mista Netanyahu zai gana da shugabannin Afrika da dama yayin ziyarar.

Masu lura da al'amura sun ce Isra'ila na son samun goyan baya daga kasashen Afrika a Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kulla huldar kasuwanci.