An salwantar da mota wajen shirya fim

Hakkin mallakar hoto kamal
Image caption Jarumi Ali Nuhu yayin da yake jefa motar a cikin kududdufi

An yi taron nuna dandanon wani fim a masana'antar Hausa ta Kannywood karon farko a tarihi.

Masu shirya fim din mai taken 'Umar Sanda,' suna bugun kirji da cewa shi ne na farko da aka salwantar da mota sukutum a yayin aiwatar da shi, don ganin an nuna zahirin yadda al'amura suka gudana gwargwadon tsarin labarinsa.

Dandanon fim din ya nuna jarumin shirin Ali Nuhu ya tsunduma motarsa cikin wani katon kududdufi a kokarin boye shaidar laifin da iyalinsa suka aikata.

Amma daga bisani bayan shirin fim din, an tsamo motar ta kuma cigaba da amfani.

Manufar nuna dandanon wannan fim, shi ne amfani da kafofin da taron ya gayyata wajen sanar da 'yan kallo yadda fim din ya kasance.

An shirya fim din Umar Sanda ne a kan wani labari wanda asalinsa na mutanen kasar Japan ne, lamarin da darakta Kamal Alkali ya ce wata bajinta ce ta masu shirya fina-finai wajen sada al'ummomi daban-daban a fadin duniya masu alakar al'adu.

Hakkin mallakar hoto kamal
Image caption Kamal Alkali ne daraktan fim din Umar Sanda

''Abin da muka kalla ga wannan labari wanda na Japan da Indiya ne kuma muka kwaikwayo shi, shi ne labari ne wanda zai iya zuwa ko ina a kalla, saboda labarin kisan kai kuma na laifi tare da 'yan sanda ne, tun da mu duk rainon Ingila ne. Za ka ga tsarin shigar da laifi da warware shi iri daya ne duk duniya. To shi ya sa ya haska rayuwar al'umma kuma an nuna son iyali ne ya janyo aka lullube laifi, wanda 'yarsa ce ta aikata shi ba mamaki,'' in ji darakta Kamal Alkali.

Masu shirya fim din Umar Sanda suna fatan irin wadannan sabbin dabaru za su bunkasa kasuwa da rage kaifin satar fasahar hazikan 'yan fim din a duniya