Natenyahu ya fara ziyara kasashen Afurka

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ziyarar ta karfafa dangantaka ce tsakanin Israela da Afurka.

Firaiministan Israela Benyamin Netanyahu ya fara ziyarar aiki kasashen Afurka domin inganta dangantaka tsakanin su.

Mr Netanyahu zai kai ziyarar ne kasashe uku a nahiyar Afurka, ya kuma tattauna da wasu daga cikin shugabannin kasashen Afurka a Uganda kai batutuwan da suka shafi tsaro.

Tun da fari ya ziyarci filin jirgin sama na Entebe, dan tunawa da wani samame da sojojin Israela suka kai tare da kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a cikin jirgi shekaru 40 da suka gabata.

A wanna lokacin ne kuma aka kashe dan uwan Mr Netanyahu Yonatan, a wata hira da yayi da gidan talabijin din kasar Uganda Netanyahu ya ce ayyukan 'yan ta'adda na janyowa koma bayan kasashe da dama.