Cinnaka ya riga mu gidan gaskiya

Hakkin mallakar hoto You tube
Image caption Cinnaka ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa wasannin barkwanci

Fitaccen dan wasan barkwancin nan na Hausa, Isma'il Bappah Ahmed [Cinnaka] ya rasu.

Wasu makusantan Cinnaka sun ce ya rasu ne ranar Talatar nan bayan ya yi fama da gajeriyar rashin lafiya a garinsu na Wudil da ke jihar Kano a arewacin Najeriya.

Marigayin ya bar mata guda da 'ya'ya shida.

Shi dai Cinnaka ya yi yayi da marigayi Rabilu Musa Dan Ibro da Yautai da makamantan su.