Za a gabatar da rahoton harin Paris

Harin birnin Paris a bara. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 150 ne suka rayukansu a harin.

Nan gaba a yau ne hukumar majalisar dokokin Faransa za su gabatar da sakamakon bincike kan hari mafi muni da aka kai a tarihin kasar a birnin Paris a watan Nuwambar bara.

Mutane dari da hamsin ne suka rasa rayukansu a harin da kungiyar masu ikirarin kafa daular musulunci a kasashen Syria da Iraqi suka dauki alhakin kai wa.

Jagoran binciken Georges Fenech ya ce manufar binciken ita ce sanin ainahin abinda ya faru, da magance faruwar hari irin sa nan gaba.

A nasu bangaren 'yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su sun tsoki lamirin jami'an tsaro da gazawa wajen maida martani, da kuma rashin maida hankalin baiwa wadanda suka jikkata taimakon gaggawa a asibitocin da aka kai su, da kuma rashin gano wadanda suka mutu.