Sallar bana ta fi ta bara armashi a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'ummar Borno na cikin walwala a sallar bana

Al'ummar jihar Borno da ke arewacin Najeriya sun ce sun yi bikin karamar sallah cikin kwanciyar hankali a bana.

Jama'a sun ce sun samu walwala sabanin irin yadda a kan yi bukukuwan sallah cikin kunci a jihar a baya, saboda dalilai na tsaro, sakamakon hare-haren Boko Haram.

Malama Fati Abubakar, ta kungiyar Like Minds, mai zaman kanta, ta ce, ''Hakika wannan sallar ta banbanta da ta 'yan shekaru da suka wuce, inda al'ummar jihar ke cikin tararradi.

Ta kuma kara da cewa duk da matsin tattalin arziki da ake ciki, kungiyoyi masu zaman kansu sun yi kokarin kai kayan tallafi kamar tufafi da abinci ga sansanonin 'yan gudun hijira.

''Duk da cewa ba za mu iya wadata kowa da abin da suke bukata ba, amma an yi kokari wajen basu tufafi musamman ga yara da kuma abinci don su ma su ji dadin sallar,'' in ji Fatima.

An shafe shekaru jihar Borno na fama da tashe--tashen hankula ta yadda al'umma basu da sukuni a kowanne yanayi ko da kuwa na hidimar sallah ne.

Amma a bana sun ce duk da halin matsin tattalin arziki da ake fama da shi, to su kuwa suna sambarka ne da zaman lafiyar da ke karuwa a jihar.