'Birtaniya ta yi kuskuren shiga yakin Iraki'

Image caption Tony Blair ya nemi afuwa kan kuskuren da ya yi

Kwamitin bincike kan rawar da Birtaniya ta taka a yakin Iraki, ya ce, tsohon Firai minista Tony Blair, ya kamba shaidun da ke nuna cewa tsohon shugaban kasar Iraki Saddam Hussain ya mallaki makaman kare dangi.

Rahoton da kwamitin ya fitar ya kuma, Mista Blair ya tura dakarun tsaro da ba sa cikin filin daga a Iraki, sannan kuma ba su shirya wa abin da zai biyo bayan yakin ba.

Shugaban kwamitin Sir John Chilcot, ya ce kutsawa Iraki da Birtaniya ta yi ba shi ne matakin karshe da ya kamata ta dauka ba.

Ya ce babu wata barazana daga Saddam, kuma bayanan sirrin da aka samu bai kunshi isasshiyar hujjar yin yakin ba.

Mista Blair dai ya nemi afuwar duk wani kuskure da ya faru, amma ban da matakin da ya dauka na shiga yakin.

Rahoton wanda ya dauki shekara bakwai ana hada shi, yana nan a kan shafin intanet na bincike na Iraki.

A shekarar 2003 ne Birtaniya ta shiga gamayyar kawancen Amurka don yakar Iraki, inda aka kashe sojojinta da yawa.