An ceto 'yan cirani 4500 a bahar Rum

'Yan cirani na neman taimako Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Yawancin 'yan ciranin sun fito ne daga kasashen Syria, daOakistan da Libya wadanda ke gujewa yaki a kasar su.

A kwana guda ma'aikatan ceto sun yi nasarar kubutar da kusan baki 'yan cirani Dubu hudu da dari biyar a tekun Bahar Rum.

Jiragen ruwan masu gadin tekun Italiya da sojin ruwan tarayyar turai da na jami'an bakin iyaka da kuma na kungiyoyin bada agaji su ne suka gano 'yan ciranin da aka yo fasakwaurin su a cikin jiragen ruwa na katako.

An dai baiwa wasu daga cikin su taimakon gaggawa saboda mawuyacin halin da suke ciki.

Dubban 'yan cirani ne ke rasa rayukansu a kokarin ketara Bahar Rum dan isa kasashen turai da ake yi wa kallon tudun muntsira.