Mataimakin jakadan Saliyo a Nigeria ya kubuta

Hakkin mallakar hoto google maps

Ofishin jakadancin Najeriya a kasar Saliyo, ya tabbatar da cewa masu satar mutane don karbar kudin fansa da suka sace jakadan Saliyo a Kaduna sun sake shi.

Amma babu tabbacin ko an biya masu satar mutanen wani kudin fansa kafin su saki Manjo Janar Alfred Nelson-Williams mai ritaya din.

Sai dai ofishin jakadancin ya tabbatar da cewa yana cikin halin lafiya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne masu satar mutanen suka sace shi a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja domin halartar bikin yaye dalibai sojoji a Jaji.