Sallah ta sa an tsagaita wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojin Syria sun ce tsagaita wutar za ta yi aiki tsawon kwana uku

Rundunar sojin Syria ta sanar da tsagaita wuta na tsawon kwanaki uku.

Sanarwar na zuwa ne a yayin da Musulmai suka fara shagulgulan bikin karamar sallah bayan kammala azumin watan Ramadan.

Kafar yada labarai ta kasar ta ce, tsagaita wutar zai yi aiki ne har zuwa tsakar daren Juma'a.

Idan har aka yi aiki da hakan, zai zamo shi ne yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko tun bayan da Amurka da Rasha suka cimma irin ta a karshen wata Fabrairu, wanda hakan ya rage tashe-tashen hankula a kasar na tsawon makonni.

Amma daga bisani yarjejeniyar da dakatar da aiki.

Har yanzu dai kungiyoyin adawa na Syria ba su ce komai ba kan batun tsagaita wutar.