Akwai yiwuwar kai hari Lagos da sallah — Amurka

Hakkin mallakar hoto mark knoller
Image caption Amurka ta ce 'yan kasarta su yi taka-tsantsan da birnin Lagos

Hukumar harkokin kasashen wajen Amurka ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar kai hare-hare wasu otal-otal da ke birnin Lagos a Kudancin Najeriya, yayin bukukuwan karamar sallah.

Hukumar ta fitar da wannan sanarwa ce a shafin intanet na ofishin jakadancin kasar na Najeriya a ranar Talata.

Ta kuma gargadi 'yan kasarta cewa su guji dadewa a wuraren shakatawa na bakin teku da kantunan sayar da abinci da ke birnin na Lagos.

Haka kuma sanarwar ta gargadi Amerikawan da ka da su yi tafiya ta jirgin ruwa zuwa sauran sassan Kudancin kasar, kana idan za su shiga gari daga filin jirgi su tabbatar sun tafi cikin ayarin motoci.

A cewar sanarwar, yanayin yiwuwar barazanar hari a lagos daya yake da na wadanda aka saba gani a yankunan da masu da'awar jihadi suka fi karfi.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Amurka ke gargadin 'yan kasarta kan yin taka-tsantsan ba don gujewa hare-hare a sassa daban-daban na duniya.